Shi kuma zai maida hankalinsa ne a neman wanda ke kashe masa mata mu kuma muna aikinmu a kansa cikin sauki, Mun gamsu mun kuma dawo gida cikin farin ciki. Tun daga nan abubuwa suka cigaba da gudana, muma muka dage, bama sanya waien kokarin shiga da fita da gain an aurama Eshaan mace bayan mutuwar wasu. Ga kuma abinda duk boka Barbushi ya fada yanata faruwa daki-daki, tako ina zaginsa ake da la'antar mulkinsa har mutane na kiransa da Fir'auna. Hakan a mana dad, shiyyasa ma muka baza yaranmu tako ina suna gano mana kyawawan matan da za'a aurama masa, da munzo muka kalame Mammah da zance musamman ni sai ta amine da fatan ALLAH yasa karshen al'amarin kenan. A haka har lissafinmu ya kai ga wasu yara da mahaifinsu ke kawo zuma masarautar nan. Wani kuma yaronmu dake mana aikine ya kawo mana zindensu ashe abokinsa ne. Mun tabbatar da auren ta farko kamar yanda aka saba itama ta mutu, kasancewar munga biyu bayanta muka sake shigewa gaba aka auro ta biyu. Itama dai ta rasun, dan haka muka dira akan ta uku. Shekarun yarinyar da wanda Barbushi ya fada ne ya samu farin cikin da fahimtar itace wadda muke nema, dan haka bayan an aurota muka fara shirya yanda zamu tarwatsa ahalinta. A wanna ranarce wanda yay mana hanyar sanin gidan yaji hirarmu (abokin nasa kenan), bamu nuna masa mun sani ba, sai muka bibiyi rayuwarsa ta hanyar matarsa. Kudi muka bata mai uban yawa da firgita mata rayuwa, harma Jasim yay amtan da ita sannan muka bata gubar data bama mijin nata sannan muka wuce. Washe gari bamu san miya faru ba ta kiramu a rikice wai mijinta ya tafi sanarma iyayen yarinyar nan komal amma ta bashi gubar da muka bata. (adsbygoogle = window.adsbygoogle []).push(); Hankalinmu ya tashi, babu sanya muka samar da yan sanda suka je gareta da ga nan tai musu jagora zuwan gidan. Anan ne muka saka aka kama mai gidan da babban dansa. (Nasan dal baku manta kama babiy da Hanash ba?)".