Wani abin lura kuma a nan shi ne za mu ga cewa wani lokaci mukan iya kasawa cikin rayuwarmu ta mutumtaka wajen nuna wadannan albarkun, mukan iya zama da kauna amma sai ka ga muna da karancin nuna hakuri, ko kamun kai da sauransu. To me ya kamata mu yi a irin wannan yanayi? Ya kamata mu girma cikin ruhaniyya ta wurin yin nazari cikin Littafi Mai tsarki, mu bincika mu ga me Ubangiji Allah Yake so mu yi cikin rayuwa mu, mu kuma yi koyi da abubuwan da ke cikin Littafi Mai tsarki, mu bi gurbin Yesu Almasihu domin shi ne hanya, shi ne gaskiya, shi ne kuma rai. Kowane wayewar gari mu roki Ubangiji Allah Ya ba mu albarkar ruhunSa mu kuma bude kofar zuciyarmu ga nufinSa, ta wurin yin haka kuwa babu shakka za mu samu nasara kuma ta wurin yin haka ne za mu nuna hasken Almasihu ga dukan duniya a zamanmu na Kirista.
Ama a hakan, wanan ba bayannuwan Yesu Christi mana ba kenan. Shi bai yi bukatan laifi domin ALLAH ya sa mu girmama ta wanan bangaskiyan ba, wato, ALLAH ba ya bukatan ayi mana laifi sanan domin mu bi kalman jumrewan sa. Shi ya zo bisa kauna ne ma ma su bin sa, wato, a sakanin su, ta zuciyan kauna, ba wanda zai mari wani, ko ya kai wani kotu, ko ya sa wani dole domin yayi wani dogon tafiya da bai so ba. Zamu kasance daya ta zuciyan kauna wa junan mu, kuma idan wani ma ya yi laifi, sai ya nima gafara, sanan ta wurin ganewa, wanda aka masa zunubin zai yafe. Aikin ma su zuciyan Yesu ne su zama ma su wakilcin Yesu ta wurin nuna gafara ma ma su zunubi, toh a hakan ne mu firistocin ALLAH.
Kokuma yanda doka na shida ya ce kadda mu yi kashi. Ama sai kuma Muhammed ya kasance a wannan halin ne har ga girman Musulunci. Toh, idan ka kashe wani, yaya ne zai zo ga tuba ko ga karbin ALLAH daga sanin sa? ALLAH bai dauki yanci zabin mu ba, ama sai mutum ne sai ya kuma kafa da wai bin ALLAH dole ne? Toh mun gan duk wanan halayen sun bayanna a cikin Muhammed domin ba shi da Ruhu mai tsarki da zai bayanna ma shi nufin ALLAH. Duka wannan ne muna ce da su bangaskiyan kai, domin bangaskiyan ALLAH na cikin alheri da rai da kauna ne, kuma a cikin wayanan ne mutani masu zunubi sun zo ga tuba, kuma suna zuwa ga tuba. Sanan kuma idan ka je ka aikata naka bangaskiyan, sai kuma mutani su ki ALLAH ta yanda halin ka mumuna ne.
Dukan sujada ya tabata ga ALLAH ne, ama damuwan shine mu na dauki ALLAH da yawan girma ko kai da shi ya tambaya da kuma ya ke. Wannan kuma mun gan yana shafi yanda mu ke tunani da yin rayuwa ta yanda ALLAH ya yi niya. ALLAH bai halice mu domin mu yi ta bauta ma sa ba ne, ya halice mu alloli (ta kasan halitan mu) domin ya gan abun da ya ke, wato shi bisa kauna da alheri.
Ya bar tsarki ma bangaskiya, dalilin mutuntakan sa kenan. Don da an bi na rayuwan tsarki sa ne, da dukan mu mun mutu ko. Ama ALLAH ya turo shi ya kuma zama bangaskiya a cikin rayuwan laifi da zunubi domin ya komar da mu rayuwan tsarki. Misali; da an bi na sa ne, wato Yesu bisa mai tsarki, wato kamin ya zama mutum, da masu son kai sun mutu. Ama ALLAH ta wurin Kalman sa, wato Yesu, ya jumre da kashe su har ga chanzawan yesu zuwa kalman bangaskiya, don ta wurin Yesu bisa kauna, ma su son kai dinnan za su kuma zama ma su bayyaswa. Toh, nasaran ALLAH kenan a kan zunubi, domin da Yesu ya dinga kashe masu son kai bisa shi tsarki, toh, da bai fiskance ALLAH ba bisa mai jumrewa ba, kuma bai fiskance cewa mutum dinnan yana iya canzawa ba.
Misali, doka ya ce wai yaro ya bar baba ya wuce kofan kamin shi, ko kuwa, idan yaro ya gan tsoho, sanan sai ya tashi ma tsohon nan ya zauna. Wanan doka ne, kuma dokan nan Yesu ne ya kafa, ama dokan nan kuma ba Yesu ba ne. Yesu kauna ne, kuma ba shi da jiki ko siffa, wato, ta zuciyan Yesu bisa gaskiya, baba ya na iya barin yaron nan ya wuce wanan kofan kamin shi, kuma tsohon nan na iya tashi ma yaro ya zauna, domin kauna ba shi da siffa ko bangare. Yesu ya kaffa dokokin bisa irin mutanin da ya ke jagorance ne, irin mutanin ma su son girma da kuma son kai ne, kuma mutanin doka ne. Ama ta wurin Yesu, wato mutumin sa, ba wani abu wai doka ama kuma dokan kauna ne.